An yi wa Sylvia fyaɗe tun tana ƴar shekara 14
- Marubuci, By Swaminathan Natarajan
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
Jamhuriyar Ɗimukraɗiyar Congo da ke yankin Afirka ita ce ƙasar da yara suka fi shan uƙuba kuma kullum yanayin na ƙara munana.
« Idan aka kwatanta da alƙaluman shekarar da ta gabata da kuma na wannan shekarar, an samu ƙarin cin zarafi mai alaƙa da jinsi kashi 47 cikin 100.
Alkalluma ne masu yawa, » in ji Sheema Sen Gupta.
Sheema Sen Gupta, darakta ce ta Asusun kula da yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, ta kuma tattauna da BBC bayan kammala wata ziyara da ta yi a sansanonin waɗanda suka rasa muhallansu a gabashi a ƙarshen watan Satumbar da ya gabata.
« Idan aka yi dubiya zuwa yankin gabashin ƙasar, Kivu ta Yamma da Kivu ta Kudu, yarinya huɗu cikin biyar ta fuskanci cin zarafi mai alaƙa da jinsi, » in ji ta.
Girman ƙasar ya kai na yammacin Turai, kuma akwai mutane miliyan 100 da ke rayuwa a ƙasar, haka kuma ƙasace da ke da albarkatun ƙasa.
A 2022, Unicef ta samu bayanai na cin zarafin yara har guda 3,400 a ƙasar ta DR Congo, daga cikin yaran, akwai yara 1,600 da aka saka cikin ƙungiyoyin ƴan bindiga, an kuma kashe 700 a rikici, yayin da aƙalla yara 290 suka fuskanci cin zarafin jima’i.
« Kasancewa ta a ɓangaren bada kariya ga yara, nasan abubuwan da ke faruwa. amman idan ka haɗu da yaran da matasan zaka shiga tashin hankali. Raina ya ɓaci sosai kan irin cin zarafin da ake wa yara. »
Tun farkon 2023, sama da mutane miliyan ne suka rasa muhallansu a DR Congo, adadin da ya sanya yawan mutanen da suka rasa muhallansu ya kai sama da miliyan 6.1.
Mata waɗanda ke zama a waɗannan sansanoni na shiga cikin haɗari a duk lokacin da suka je neman ruwa.
Tashin hankali da rikice-rikice
Rikicin ya ɓarke ne shekaru 30 da suka gabata, lamarin da ya yi sanadin mutuwar sama da mutane miliyan shida.
A bara rikice-rikice sun ƙara ƙazancewa kasancewar jami’an tsaro na ƙoƙarin yaƙi da ƙungiyoyin masu ɗauke da bindiga sama da 100 a gabashin ƙasar.
Hakan na faruwa ne kuwa duk da dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da aka jibge ƙasar.
Ƙungiyar ƴan tawaye ta M23 ta riƙa kama yankunan ƙasar tun a cikin watan Fabarairu.
An kafa ƙungiyar ce shekaru 10 da suka gabata, inda take iƙirarin kare muradun ƴan ƙabilar Tutsi mazauna Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo daga mayaƙan ƙabilar Hutu.
Ƙasar Kongo na zargin Rwanda da goyon bayan ƙungiyar.
Mutanen da ake tursasa wa barin ƙauyukansu kan ƙare ne a manyan sansanoni kamar wanda ake kira sansanin Rhoe, wanda Sen Gupta ta ziyarta.
Sansanin ya na a nisan kilomita 45 ta arewa maso gabashin garin Bunia, babban birnin yankin, wanda dakarun MDD ke bai wa tsaro.
Sai dai duk da haka yara mata a garin na cikin hatsari.
Sylvia (wadda muka ɓoye sunanta) ƴar shekara 16 ce amma yanzu haka tana da ɗa mai watanni goma da haihuwa, kuma ta samu cikinsa ne bayan an yi mata fyaɗe.
BBC ta tattauna da ita da ita gaban malaminta, ta hanyar mai tafinta na asusun Unicef.
Ta shaida wa BBC cewa: « Lokacin da nake dawowa daga wurin ɗebo ruwa, sai aka far mani a cikin sansanin. »
« Abin ya faru ne daidai lokacin da rana ke faɗuwa. Ban san wane ne ya far mini ba saboda duhu ya fara. »
Asusun Unicef ya ce sama da mutane 70,000 ne ke rayuwa a sansanin Rhoe cikin yanayi maras kyawu
Bayan faruwar fyaɗen, mutane sun zo sun zagaye ta amma babu wanda ya iya taimakonta.
Tana tunanin cewa wanda ya yi mata fyaɗen yana nan cikin sansanin yana harkokinsa.
Ta ce « Ina cikin takaici, kuma a tsorace nake. Duk yara ƴan sama da shekara 10 a tsorace suke saboda rashin tsaro. »
Bayan kwashe shekara uku, yanzu ta koma makaranta, kuma ana ba ta shawarwari.
Sylvia ta ce « Mamata ce take kula da jaririyar idan na taho makaranta. Idan kuma na tafi gida sai na ci gaba da kula da ita. »
Bukkar da Sylvia ke zama an haɗa ta ne da gora da yunɓu, sannan an rufe saman da leda. Babu lantarki kuma mutane 50 ne ke amfani da ban-ɗaki guda.
Sylvia ta ci gaba da cewa « babu tsaro da zarar dare ya yi. Kuma babu isasshen abinci. »
« Ba ni da mahaifi, ina zama ne tare da mahifiyata. Ba mu da wani namiji wanda zai kare mu. Hakan ya sa zuwa neman ruwa da zarar yamma ta yi yake zama mai haɗari. »
An bai wa Sylvia shawarwari shi ya sa ba ta nuna ƙiyayya ga jaririyar da ta haifa ba.
Mata da yara waɗanda ba su da namiji wanda zai ba su kariya suna cikin hatsari a sansanin
Jaririyar na ta gwalan-gwalan yayin da nake magana da mahaifiyar Sylvia, Georgina.
Georgina mai shekara 40 ta ce « Wiale na cikin ƙoshin lafiya, tana son wasa da kuma fahimtar abubuwa. »
Georgina na samun kuɗin kashewa ne ta hanyar yin aikatau. Mijinta ya rasu saboda haka ba ta da kowa.
Georgina ta ce « abu ne mai matuƙar wahala ga Sylvia ta kula da ɗiyarta. Har yanzu ita ma yarinya ce. »
Rayuwa kan siraɗi
Ƴan bindiga ne suka tarwatsa Sylvia da mahaifiyarta daga ƙauyensu shekaru uku da suka gabata lokacin da aka kai hari.
Yanzu ba su san lokacin da za su sake komawa gida ba.
Georgina ta ce: « sau da yawa Sylvia na yin fushi. Takan tuna da harin da aka kai mana a kai-a kai, wani lokaci takan shiga cikin damuwa. »
Shugaban makarantar da ke sansanin, Lonu Bauojo Innocent ne ya ƙarfafa wa Sylvia gwiwa wajen ganin ta koma makaranta.
Ya ce « akwai yara da ke cikin hali irin nata da yawa. Tana da ƙoƙari sosai kuma rayuwarta za ta iya komawa daidai idan ta ci gaba da zuwa makaranta. »
Kasancewar an fi yi wa yaran fyaɗe ne a lokacin da suka je ɗibar ruwa idan yamma ta yi, yanzu an samar da sabbin tankunan ruwa domin rage haɗarin da suke faɗawa ciki.
Haka nan kuma a yanzu mata sukan yi ƙungiya ne idan za su je ɗiban ruwa domin samar wa kansu tsaro.
Sen Gupta sanye da shuɗiyar riga ta tattauna da waɗanda suka fuskanci cin zarafi ta hanyar lalata a sansanin
Sai dai rayuwar gaba ɗaya wahala ce. Babu ƴan sanda a sansanin waɗanda za su kare ko kuma su yi bincike kan cin zarafi na lalata.
Kuma gwamnatin Jamhuriyar Demokuradiyyar Kongo ta umurci dakarun Majalisar Dinkin Duniya wadanda ke bai wa sansanin kariya wa’adin su fice daga ƙasar nan da ƙarshen shekara.
Dakarun na MDD na fuskantar fushi daga al’umma saboda gazawarsu wurin bai wa al’umma kariya.
Sen Gupta na sa ran ƙasar za ta ci gaba da samar da tsaro a sansanin.
Lamri ne da ya zama ruwan dare a faɗin duniya, a kodayaushe ana samun rahotannin cin zarafi na lalata a sansanonin waɗanda rikici ya tarwatsa.
« Yana da wahala ka iya cewa ko matsalar fyaɗe na ƙara munana, sai dai akwai lokutan da ake bayyana cewa an samu hauhawar yawaitar cin zarafin lalata a sansanonin,: in ji Sen Gupta.
« Mun san cewa lamarin ya ƙazance a Kongo, matsalar ƙaruwa take yi. »
Syliva na jin daɗin karantun da take yi kuma tana fatan wata rana ta yi aiki da wata ƙungiyar bayar da agaji
Lamarin babu daɗi ga waɗanda suka fuskanci cin zarafi na lalata, amma akwai alamun kaɗan na haske a gaba.
Sylvia na halartar sabbin ajujuwan da aka gina a makarantar wadda take kusa da sansanin.
Yanzu makarantar na da ajujuwa uku, kuma ana gina wasu guda huɗu.
« Ina koyon karatu sosai. Ina jin daɗin zuwa makaranta tare da ƙawayena. »
Crédit: Lien source


Les commentaires sont fermés.