Wani rahoton kungiyar fararen hula ta Tarayyar Turai ya ce Hukumar zaben Jamhuriyar Dimkaradiyyar Congo ta gaza bada bayani a kan yadda ta kashe kudaden da ta karba daga gwamnatin kasar, kana ta bada kwangilar sayen kayayyaki marasa kan gado.
Wallafawa ranar:
Minti 1
Rahoton ya ce hukmar zaben kasar, wato CENI ta gamu da matsalar gibi a kasafin kudinta, batun da ya zame wa gwamnatin shugaba Felix Tshisekedi karfen kafa.
Rahoton, wanda aka samar da shi sakamakon wani Nazari da cibiyar bincike a kan kudaden al’umma da ciki gaban kasa ya yi, ya ce hukumar zaben ya karbi kudaden da suka kai dala biliyan daya da miliyan 100 a tsakanin shekarar 2021 daa 2023.
Ya kuma bukaci bangaren shari’ar Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ta kaddamar da bincike a kan yadda hukumar zaben kasar ta sarrafa kudaden da aka bata don gudanar da zabuka.
Hukumar zaben ba ta ce uffan ba duk da bukatar da manema labarai suka mika ma ta na mayar da martani, haka ma bangaren gwamnatin kasar.
Matsalolin da suka shafi tutsun na’ura, bacewar kayayakin zabe da kuma dage zaben na watan Disamba bagatatan ne suka yi wa zaben dabaibaiyi, lamarin da ya sa dan takarar babbar jam’iyyar adawa ya yi zargin tafka magudi a zaben, yana mai kira a sake shi.
Crédit: Lien source


Les commentaires sont fermés.