Watanni shida bayan kama dan jarida Stanis Bujakera ,a yau juma’a masu gabatar da kara sun bukaci daurin shekaru 20 a gidan yari yan lokuta da kawo karshen zaman kotu a Kinshasa. Ana tuhumar sa da rubuta labarin da ke tonon silili da kuma barrazana ga ayukan soji biyo bayan mutuwar wani dan adawa.
Wallafawa ranar:
Minti 1
A zaman na yau, mai gabatar da kara Serge Bashonga ya bukaci kotu ta zartas da hukunci mai tsanani wanda hakan zai zama abin koyi ga jama’a na kaucewa yada labaren jabu da kan iya tayar da hankali da kuma janyo tashin hankali cikin jama’a.
Nan take tuhumar mai gabatar da kara ya biyo bayan karar da masu kare dan jaridar suka yi, wanda ke adawa da duk tuhume-tuhumen da ake yi wa Stanis Bujakera.
Maitre Papy Niango mai kare dan jaridar cikin juyayi ya na mai rokon kotu da ta yi adalaci, inda ya karasa da cewa »Idan kuka janye tuhumar,za ku wanke shi,wanda hakan zai yi kuma tasiri a wannan lokaci na mulkin farrar hula.
Stanis Bujakera da karamatr murya ya na mai cewa »Ina neman a wanke ni gaba daya. A karshe kotun ta tsaida ranar 20ga watan Maris na wannan shekara ,za ta sanar da hukuncin da ya dace ta zartas ga wannan dan jarida.
Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International, ta yi kiyasin cewa an kama dan jaridar ne « bisa zarge-zargen karya », ta sake yin kira a yau Juma’a, na ganin a sake shi cikin gaggawa.
Crédit: Lien source


Les commentaires sont fermés.