Afrika ta kudu za ta aika dakaru dubu 2 da 900 Congo don yakar M23

Afrika ta kudu na shirin aikewa da dakaru dubu 2 da 900 zuwa Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo karkashin kungiyar kasashen kudancin Afrika don fara aikin wanzar da zaman lafiya a kasar mai fama da tarin matsalolin tsaro.

Wallafawa ranar:

Minti 1

Sanarwar da Afrika ta kudun ta fitar ta ce aikin dakarun na shekara guda da ya faro daga ranar 15 ga watan Disamban bara zuwa 15 ga watan Disamban shekarar nan zai lakume kudi rand biliyan 2 dai dai da dala miliyan 105.75.

A watan Mayun bara ne kungiyar kasashen kudancin Afrika mai mambobi 16 ta amince da aike dakaru Congo don fara aikin wanzar da zaman lafiya bayan da kasar ta kawo karshen zaman dakarun Majalisar Dinkin Duniya da na kungiyar gabashin Afrika wadanda ke makamancin aikin a baya.

Fiye da shekaru 10 yankin gabashin Congo ya shafe ya na fama da matsalolin tsaro wanda ya raba iyalai akalla miliyan 7 da muhallansu.

Congo mai arzikin mai arzikin ma’adinan Cobalt kuma mafi fitar da jan gaji kasuwannin duniya ta amince da shigar dakarun na Afrika ta kudu ne bayan janyewar dakarun tsakiyar Afrika da kuma na Majalisar Dinkin Duniya daga cikinta.

Hadakar dakarun da Afrika ta kudun za ta tura sun kunshi na kasashen Malawi da Tanzani wadanda za su taimaka wajen kange barazanar M23.

Crédit: Lien source

Les commentaires sont fermés.