Rahotanni daga yankin na nuni cewa da misalin karfe 9 na safe agogon kasar (8 na safe agogon GMT) gobara ta tashi a makarantar sakandare ta Mwanga, makarantar Katolika da ke Kolwezi, a lardin Lualaba (yankin Katanga).
Gobarar, wacce har yanzu ba a san ko mai ya haifar da ita ba , ta faro ne daga makarantar kwana, sannan ta lalata gine-ginen makarantun firamare da sakandare.
Sheidu sun bayyana cewa domin cira da rayyukan su « dalibai sun yi tsalle daga rufin ginin », tsayin « mita uku », labarin da Yarima Timothée, wani shaida, da aka samu ta wayar tarho a Lubumbashi, babban birnin tattalin arzikin kasar ya tabbatarwa manema labarai da AFP. Ya kara da cewa da dama daga cikinsu “sun karye” gabobin.
A cikin wani faifan bidiyo da ya fara yaduwa cikin sauri a shafukan sada zumunta, ana iya ganin matasa dalibai sanye da kayan aiki suna tsalle-tsalle cikin ruf da ciki daga rufin ginin makarantar da ke kona.
Akalla dalibai 97 ne aka kwantar da su a asibiti, ciki har da kusan 30 da suka samu karaya a wasu asibitocin cikin gida guda hudu, kamar yadda wani jami’in sadarwa na gwamnatin lardin Lualaba ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP, ya kara da cewa ba a samu rahoton mutuwa ba.
Crédit: Lien source


Les commentaires sont fermés.