« Ina tunanin za a zabe ni a zagayen farko »- Firaministan Senegal Amadou Ba

Amadou Ba, wanda aka zaba a watan Satumban da ya gabata a matsayin dan takarar jam’iyyar hadaka ta Benno Bokk Yakaar mai mulki don maye gurbin Macky Sall, ya yi imanin cewa yana da « gata na kasancewa cikin kawance mafi karfi, mafi tsari ». Don haka ya ce, “babu shakka a nasa ra’ayi za su tsallake zuwa zagayen farko.

Wallafawa ranar:

Minti 1

A kasar ta Senegal daga ciki yan takara,dan takara Karim Wade ya zargi Firaministan kasar da kasancewa wanda ya ingiza kin amincewar takararsa daga majalisar tsarin mulkin kasar na ranar 20 ga watan Janairu 2024.

Sai dai Firaministan ya musanta haka,wata guda gabanin zaben shugaban kasa, dan takara na da matukar kwarin guiwa kan yiwuwar samun nasara, Amadaou Ba ya na mai bayyana cewa ya auna ma’auni da girman ci gaban da aka samu a karkashin jagorancin Shugaba Macky Sall.

Zaben kasar Senegal © Studio graphique FMM

 Ya dau alkawalin ganin ya samar da aikin yi ga matasa, musamman wadatar da wutar lantarki ga kowa da kowa da kuma ingantattun hanyoyi.

Game da daruruwan ‘yan adawa masu goyon bayan Ousmane Sonko waɗanda aka daure tun tarzomar Maris 2021 da Yuni 2023, dan takarar firaminista kuma dan takara ya dau alkawali idan an zabe shi, zai hanzarta duk hanyoyin shari’a » da « daidaita ‘yan Senegal ».

Jami'in hukumar zaben Senegal
Jami’in hukumar zaben Senegal AFP – MICHELE CATTANI

A karshe, game da makomar CFA franc, tsohon ministan kudi na Macky Sall kuma Firaminista ,dan takara ya yi imanin cewa gyara ya zama dole, amma ba tare da fadawa cikin rudani ko neman suna.

 

Crédit: Lien source

Les commentaires sont fermés.