Kungiyar ci gaban Tattalin Arzikin Kasashen Tsakiyar Afirka ta amince da janye takunkumin da ta kakabawa Gabon a ranar Asabar din da ta gabata, tare da mayar da ita cikin kungiyar kasashen yankin, watanni shida bayan dakatar da ita, a matsayin martani kan juyin mulkin da ya hambarar da shugaba Ali Bongo.
Wallafawa ranar:
Minti 1
Ministan harkokin wajen Gabon Regis Onanga Ndiaye, ya bayyana hakan a wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin a yammacin Asabar, inda ya ce matakin ya biyo bayan taro da mambobin kungiyar suka yi a makwabciyarsu Equatorial Guinea.
Babu wata sanarwa da kungiyar ta fitar, sai dai a wani sakon da ya wallafa ta shafinsa na X ministan harkokin wajen Burundi Albert Shingiro ya tabbatar da yarjejeniyar dage takunkumin da aka cimma a taron da ya halarta.
Juyin mulki
Jim kadan bayan juyin mulkin da aka yi a ranar 30 ga watan Agusta, kungiyar ta dakatar Gabon daga cikinta da kuma shiga duk wasu harkokin da ke da alaka da ita – matakan da ta ce za su ci gaba da aiki har sai an dawo da tsarin mulkin kasar.
Ita dai gwamnatin mulkin sojan da ta hambarar da Bongo har yanzu tana kan karagar mulki, amma a watan Nuwamba ta ce tana da burin gudanar da zabe a watan Agustan 2025.
Crédit: Lien source


Les commentaires sont fermés.