Asalin hoton, Getty images
Ivory Coast mai masaukin baƙi za ta fafata da Najeriya a matakin rukuni a gasar cin kofin nahiyar Afirka inda aka hada su a rukunin A.
Ƙasar wanda ta lashe gasar a 1992 da 2015 za ta buɗe gasar ne a ranar 13 ga watan Janairu inda za ta kara da Guinea-Bissau, yayin da Equatorial Guinea za ta kasance ƙungiya ta hudu a rukunin.
Senegal mai rike da kofin Afirka za ta fafata da Kamaru a matakin rukuni na gasar, zakarun na nahiyar Afirka sun fito ne a rukunin C, inda za su kara da makwabtansu Gambia da kuma Guinea.
Ƙasar da ta kai wasan kusa da na ƙarshe a gasar cin kofin duniya da kuma mai masaukin baƙi a shekarar 2025 Morocco za ta kara da DR Congo a matakin rukunin F, Zambia da kuma Tanzania.
Za a yi amfani da filayen wasa guda biyu a Abidjan babban birnin ƙasar Ivory Coast, da ɗaya a Bouake da wasu sabbin filayen wasa guda uku da aka gina a Korhogo da San Pedro da kuma Yamoussoukro domin gudanar da gasar.
Yadda rukunan suka kasance
Runinin A: Ivory Coast, Nigeria, Equatorial Guinea, Guinea-Bissau.
Rukunin B: Egypt, Ghana, Cape Verde, Mozambique.
Rukunin C: Senegal, Cameroon, Guinea, The Gambia.
Rukunin D: Algeria, Burkina Faso, Mauritania, Angola.
Rukunin E: Tunisia, Mali, South Africa, Namibia.
Rukunin F: Morocco, DR Congo, Zambia, Tanzania.
Za a fara gasar wadda ta ƙunshi ƙasashe 24 daga ranar 13 ga watan Junairu zuwa 11 ga watan Fabrairun shekara ta 2024
Crédit: Lien source


Les commentaires sont fermés.